Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Kasar Habasha tana wakiltar babbar dama ga ci gaban tattalin arzikin kasarsa
Kakakin Majalisar shawarar Musulunci ta Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya yi la’akari da cewa: Kasar Habasha, ta hanyar kungiyar BRICS, tana wakiltar wata babbar dama ce ga ci gaban tattalin arzikin kasarsa a karkashin munanan matakai da Iran take fuskanta na takunkumai.
A yau alhamis, kafin ya wuce zuwa kasar Habasha, Qalibaf ya bayyana imaninsa cewa: Daya daga cikin muhimman damammaki shi ne nahiyar Afirka, yana mai nuni da cewa: Ziyararsa zuwa kasar Habasha ta zo ne saboda wannan kasa tana da cikakkiyar alkibla, don haka ta shiga kungiyar BRICS tare da Iran, Saudi Arabiya da Masar.
Ya bayyana cewa, kasar Habasha ita ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen samun ci gaba, inda ya kara da cewa: Habasha na da muhimmin matsayi a nahiyar Afirka.