Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Babu wani sauyi a akidar Shirin makamashin nukiliyar kasar Iran
Sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadian ya bayyana a yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Oman, Badr al-Busaidi ya jaddada cewa: Babu wani sauyi a akidar Shirin makamashin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na zaman lafiya.
A cikin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi la’akari da dogon tarihin dangantakar da ke tsakanin kasashensu, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da ci gaban da aka samu a yankin Gabas ta Tsakiya, inda suka mai da hankali kan inganta dangantakar da ke tsakaninsu a fannoni daban- daban da suka hada da siyasa, tsaro da tattalin arziki. Sun kuma jaddada aniyarsu ta aiwatar da kyautata tsarin zirga-zirga a tsakanin kasashen biyu da ma kasashen tsakiyar Asiya da Rasha.
Sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadian, ya kuma jaddada cewa: Bayanai marasa tushe da jita-jita da suka shafi Iran na kara yawan sinadarin Uranium da kara yawan tace shi, maganganu ne marasa tushe ballantana makama, kuma har yanzu Iran na ci gaba da kiyaye tsarin da aka cimma da ita na zaman tattaunawan birnin Muscat fadar mulkin kasar Oman, yana kan daya bangaren ya yi aiki da hakkin da ya hau kansa.