Iran Ta Bayar Da Shawarar Kafa Bankin Hadin Gwiwa Na Kasashen Kungiyar Shangai

 Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a

 Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a kungiyar Shangai.

Muhammad Riza Farzin ya isa kasar ta China ne domin halartar taron gwamnonin manyan bankunan kasashen da suke mambobi a cikin wanann kungiya, domin yin nazarin hanyoyin aiki tare a tsakaninsu da kuma musayar kudade.

Muhammad Riza Farzin ya kuma kara da cewa; Daga cikin ajandar taron kungiyar a China, akwai tattauna batun kafa bankin hadin gwiwa wanda daga cikin ayyukansa a akwai aiwatar da hada-hadar kudade da mu’amala a tsakanin Bankuna.”

Gwamnan babban bankin na Iran ya bayyana cewa, wannan kungiyar tana da matukar muhimmanci, domin tana kunshe da kasashe goma daga cikinsu akwai kasashe masu tattalin arziki a duniya, kamar China, India, da Rasha. Kuma mutanen da suke cikin kasashen kungiyar suna kai kaso 45% na jumillar mutanen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments