Iran : Shugaba Pezeshkian Zai Ziyarci Iraki, A Ziyararsa Ta Farko Zuwa Ketare

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai ziyarci makwabciyar kasar Iraki a wata ziyara da zata kasance karo na farko a kasar tun bayan hawansa karagar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai ziyarci makwabciyar kasar Iraki a wata ziyara da zata kasance karo na farko a kasar tun bayan hawansa karagar mulki a watan Yuli.

Shugaba Pezeshkian wanda zai jagorantar wata babbar tawaga zai tashi zuwa Bagadaza ranar Laraba don tattaunawa da manyan jami’an Irakin.

Ziyarar ta shugaban na Iran za ta zo ne bisa gayyatar firaministan Iraki Mohammed Shi’a al-Sudani.

An bayyana cewa, kasashen biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kuma harkokin tsaro.

An sanya hannu kan yarjejeniyoyin ne a lokacin da shugaban kasar Iran Mirigayi Ibrahim Raeisi ya shirya kai wata ziyara kasar Iraki.

Ana sa ran zai gana da manyan jami’an Iraki da suka hada da shugaban kasar Abdul Latif Rashid, firaminista Al Sudani da kakakin majalisar dokokin kasar Mohsen Al-Mandalawi.

Ana kuma sa ran shugaban zai je Erbil, babban birnin yankin Kurdistan, bisa gayyatar da shugaban yankin Nechirvan Barzani ya yi masa a hukumance, tare da tattaunawa da mahukuntan Kurdawa a can.

Ana kuma sa ran zai ziyarci wani babban birnin Kurdawa Sulaymaniyeh da ke arewacin Iraki.

Jakadan na Iran a Iraki, ya yi ishara da cewa ziyarar ta Pezeshkian a Bagadaza za ta kara fadada alaka ta siyasa, tattalin arziki da al’adu tsakanin kasashen biyu.

A cikin watan Maris na 2023, ne Iran da Iraki suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro a Baghdad wanda ya kunshi hada kai wajen kare kan iyaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments