Burgedia Janar Gholamreza Jalali shugaban rundunar kare fararen hula na kasar Iran ya bayyana cewa shirin JMI na garkuwan kare kasar daga makaman maikya daban daban ne suka tilastawa HKI da Amurka dakatar da farwa kasar da yaki har zuwa yanzun.
Labarin ya nakalto Janar Jalali yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a wani taro a kudancin kasar a yau Litinin. Ya kuma kara da cewa, JMI ta sami nasarar dakatar da wadan nan makiya daga farwa kasar da yaki ya zuwa yanzu ne saboda shirin kariyan da kasar take da shi da kuma nunawa makiya irin asarar da zasu yi idan sun kuskura sun farwa kasar da yaki.
Jalali ya yi wannan maganar ne a dai dai lokacinda kasar Amurka ta kawo manya-manyan jiragen yakin kasar kusa da kasar Iran a cikin tekun Omman da tekun india don tsoratar da kasar Iran. Da kuma gargadinta kan yiyuwar fara yaki da ita.
Kafin haka dai gwamnatin shugaba Trump tana maganar sauya shugabanci a kasar Iran, tare da dawo da tsarin sarauta wanda take biyayya gareta shekaru kimani 50 da suka gabata.
Jalali ya bayyana cewa Amurka tana da manufofi 3 a wannan zuwan nata kan kasar Iran, tilasta mata dawowa kan teburin tattaunawa, kai wasu takaitaccen hare hare a cikin kasar wanda ba zai kallafa mata dukiya mai yawa ba da kuma sharer fage na samar da tashe tashen hankula a yanking aba daya.