Iran, Saudiyya Sun Bukaci A Rubanya Kokari Wajen Kawo Karshen Laifukan Isra’ila A Gaza

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Saudiyya sun amince da cewa, akwai bukatar dakatar da laifukan da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa da kuma kai

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Saudiyya sun amince da cewa, akwai bukatar dakatar da laifukan da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa da kuma kai kayan agaji ga al’ummar zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Lahadi, Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da takwaransa na Iran Abbas Araqchi, sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da ke faruwa a zirin Gaza, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi kan al’ummar Gaza, da haifar da  tashe-tashen hankula a yankin.

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Saudiyya sun kuma bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana kan turba mai kyau, inda suka tattauna kan yadda za a kara inganta wannan dangantaka a fannoni daban daban.

Araqchi da bin Farhan sun bayyana muhimmancin ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu wanda zai kasance mai amfani ga Tehran da Riyadh da ma yankin baki daya.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadin da ta gabata, Araqchi ya ce ci gaba da karfafa ayyukan na hadin gwiwa tsakanin dukaknin al’ummomin yankin gabas ta tsakiya, domin ci gaban kasashen yankin da kuma samun zaman lafiya mai dorewa, na daga cikin manyan ajandodin gwamnatin kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments