Iran, Lebanon, Iraki, Yemen sun fara atisayen hadin gwiwa na goyan bayan Gaza

Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin

Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila.

An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya.

Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin.

Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila.

A yayin faretin, an nuna tutar Falasdinu, sannan aka kona tutar Isra’ila a mashigin tekun Farisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments