Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya ce gudanar da zaben raba gardama da ya hada dukkanin Palasdinawa shi ne kadai mafita ta dimokiradiyya ga al’ummar Palasdinu.
Aref ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wajen babban taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka yi a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya a wannan Litinin.
Ya ce Iran ta ba da shawarar gudanar da zaben raba gardama tare da halartar dukkanin Falasdinawa, da suka hada da Musulmi, Kirista da Yahudawa bisa ka’idar “Kowane Bafalasdine, kuri’a daya.”
Ya kara da cewa wannan shawara za ta maido da hakkin Palasdinawa na tantancewa da kuma fayyace makomarsu.
Har ila yau Iran ta yi imanin kaucewa rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen musulmi a matsayin wata babbar dama ta tinkarar makirce-makircen da ake kitsawa duniyar musumi a wannan zamani, in ji Aref.
Mataimakin shugaban na Iran ya ce dukkanin kasashen musulmi da na larabawa ya rataya a kansu da su dauki wani kwakkwaran mataki na bai daya da nufin dakile laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan Falasdinawa da mamayar kasarsu.
Ya ce dole ne kasashen musulmi da na larabawa su bullo da hanyoyi da su tabbatar cewa ba a kara maimaita irin wadannan laifukan yaki na Isra’ila ba, tare da biyan diyya ga al’ummomin Palastinu da na Lebanon.
Aref ya ce Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin sulhu ba su da ikon kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu da kuma kai hare-hare kan al’ummar Lebanon saboda irin goyon bayan da Amurka da wasu kasashen yammacin Turai ke ba wa gwamnatin Harammtacciyar kasar Isra’ila.