Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmael Baghaie ta bayyana gazawar kungiyoyin kasa da kasa da kuma kwamitin sulhu na MDD wajen dakatar da kisan kare dangin, da ake wa al’ummar Gaza sakamakon cikakken goyon bayan da Amurka ke ba wa gwamnatin sahyoniyawan.
Jami’in diflomasiyyar na Iran ya bayyana lamarin da abun kunya, inda ya yi kira da a dauki matakin gaggawa daga al’ummar duniya don dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma gurfanar da jagororin gwamnatin mamaya bisa aikata munanan laifuka.
Mista Baghaie yayi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawa ta kai kan gidaje da tantunan Falasdinawa ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, ciki har da sansanin al-Nuseirat, wanda ya yi sanadin shahada da raunata wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan yara.
Babban jami’in na Iran ya tunatar da cewa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayar da umarnin gurfanar da wasu manyan jami’an Isra’ila bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama tare da jaddada alhakin da ke wuyan kasashe mambobin kotun na aiwatar da sammacin.