Iran: Kauyuka 3 Sun Shiga Cikin Wuraren Bude Ido Na Duniya

Kauyukan kasar Iran guda uku, Soheili a kan tsibirin Qeshm, da Kandelous a lardin Mazandaran, da kuma Shafiabad a lardin Kerman na kasar Iran sun

Kauyukan kasar Iran guda uku,  Soheili a kan tsibirin  Qeshm, da Kandelous a lardin Mazandaran, da kuma  Shafiabad a lardin Kerman na kasar Iran sun shiga cikin zababbun  kauyuka a duniya na yawon shekatawa saboda kyauwunsu da kuma samar da dukkan abin kyautata rayuwa a cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan al-adu na kasar Iran yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a.

Anoushirvan Mohseni-Bandpei, ya kara da cewa zabar wadan nan kauyuka na kasar Iran cikin kyauyuka wadanda suka cancanci shiga wuraren yawon shakatawa a duniya wanda hukumar  ‘ The United Nations World Tourism Organization (UNWTO), ta yi zai bunkasa yawon shakatawa a kasar Iran , kuma ma’aikatarsa tana aiki dare da rana don kara yawan irin wadan nan kauyuka a kasar saboda bunkasa matun yawan shahtawa a kasar da kuma ga masu zuwa yawon shakatawa a Iran daga sauran kasashen duniya.

Mataimakin ministan ya kara da cewa Iran ta shiga gasar samar da irin wadan nan kauyuka da wasu kasashe na kimani shekaru 5 da suka gabata, inda daga karshe ta sami nasarar shigar da wadan nan kauyka cikin wannan tsarin na yawon shakatawa. Kafin haka dai kauyukan Kandovan da kuma Esfand suka cikin wannan tsarin na yawon shekatawa.  Ya kuma kammala da cewa a halin yanzu akwai wasu kauyuka guda 8 a cikin kasar Iran wadanda hukumar ta UNWTO take bincike don tabbatar da cewa sun cika sharuddan shiga cikin kasashen.

Hukumar ta zami Soheili don yanayin da na kurmi. Kandelous kuma bukukuwan da suka hada kawata rakuma da sauransi. Saikuma Shadiabad sabada nauin gidagen kauyen masu kayatarwa. Da jan hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments