Iran: Janar Hussain Salami Ya Ce Babu Wani Sojon Kasar Iran Da Ya Rage A Kasar Siriya A Halin Yansu

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci (IRGC) a nan Iran Janar Hussain Salami, ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani sojan JMI

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci (IRGC) a nan Iran Janar Hussain Salami, ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani sojan JMI a kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jnar Salami yana fadar haka a jiya Talaga a gaban majalisar dokokin kasar a nan Tehran, a lokacinda majalisar ta kira shi don sauraron bayani kan yadda aka yi gwamnatin shugaba Bashar Al-asad ta fadi.

Taron wanda aka yi ba tare da yan jaradu ba, ya sanya Janar Salami a matsayin babban mai Magana a cikinsa.

Daga karshe Janar Hussain Salami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran, masu bada shawara, suna tare da shugaba Asad har zuwa lokacinda gwamnatinsa ta Fadi, ya kuma bar kasar. Amma a halin yanzu babu wani daga cikin sojojin Iran masu bada shawara da suka rage a kasar.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments