Iran: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ziyarci Kasuwar Baje Kolin Littafai A Nan Tehran

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullah Sayyid Aliyul Khaminaee ya ziyarci kasuwar baje kolin littafai wanda ke gudana a halin yanzu

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullah Sayyid Aliyul Khaminaee ya ziyarci kasuwar baje kolin littafai wanda ke gudana a halin yanzu a nan birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyanan cewa jagoran tare da tawagarsa sun isa kasuwar wanda yake gudana‘a masallacin’ Imam Khomaini (q) dake tsakiyar Tehran a safiyar yau. Kuma kamar yadda ya saba ya zagaya rumfuna da dama inda yake duba sabbin liffan da aka kawo.

Wannan dai shi ne kasuwar baje kolin littafai na kasa da kasa karo 35 inda kamfanonin bukawa da watsa littafai ko kuma saida su kimani 60 daga kasashen waje, dakuma wasu daruruwa daga cikin gida ne suke baje kolin abubuwan karatu da na koyarwa da suka kawo kasuwar.

A ranar Laraban da ta gabata ce aka bude kasuwar kuma tana ci har zuwa ranar 18 ga watan Mayun da muke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments