Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar zagayowar lokacin bukukuwan Nowruz na sabuwar shekarar hijira shamsiyya da ake amfani da itya a hukumance a kasar Iran.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa al’ummar kasar ta gidan telebijin na murnar shiga sabuwar shekara ta Farisa a yammacin wannan Alhamis.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada bukatar gwamnati da al’ummar kasar su ci gaba da zuba jari don karfafa azamarsu wajen tunkarar takunkumai na zalunci da masu girman kai na duniya suka kakaba ma kasar.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa samar da kayayyaki na samun bunkasuwa ne idan aka ba da tallafin jari mai karfi.
Jagoran ya kuma yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila da take kaiwa Gaza, inda ya yi kira ga kasashen duniya baki daya da su nuna adawa da laifukan da Amurka da Isra’ila ke aikatawa a Gaza.
A yayin da ya koma kan batun kasar Yemen, Ayatullah Khamenei ya bayyana hare-haren da Amurka ke kai wa al’ummar kasar Yemen a matsayin wani laifi da ya zama wajibi a dakatar da shi.
Ya bayyana fatan alheri, nasara, da alheri ga al’ummar musulmi a cikin sabuwar shekara.