Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da irin sadaukarwar da babban kwamandan yaki da ta’addanci na Iran Laftanar Janar Qassem Soleimani ya yi musamman wajen karfafa kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya.
“Dabarun shahid Soleimani a kodayaushe su ne farfado da ‘yan gwagwarmaya,” in ji Jagoran.
Jagoran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da gungun iyalan shahidai da mayaka da kuma masu fafutukar tsayin daka gabanin cikar shakara biyar da shahadar Janar Soleimani.
Jagoran ya bayyana rawar da Janar Soleimani ya taka a yaki da ta’addanci a matsayin “mara misali” kuma ya ce sadaukarwa da ayyukansa “dole ne su ci gaba da kasancewa abun koyi.”
Ayatullah Khamenei ya ce wata muhimmiyar sifa ta Janar Soleimani ita ce tantance al’amuran kasar tare da mahangar duniya.
Marigayi Janar Shahid Qassem Soleimani, kwamandan dakarun Rundunar Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) na Iran, ya kasance wata alama ta tsayin daka da kuma abin alfahari na kasa ga Iraniyawa da dama.
Janar Soleimani, kwamandan dakarun Quds na Iran tare da Abu Mahdi al-Muhandis, babban kwamandan rundinar Hashdu Sha’abi ta Iraki na biyu sun yi shahada ne tare da abokansu a wani harin jirgin yakin Amurka da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya bada umurni a ranar 3 ga Janairun 2020 a Iraki.