Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na kasar Saudiya da kuma shugaban asusun lamuni ta duniya wato IMF.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin JMI dai tana kokarin ganin ta kyautata dangantaka ko ta ina da kasashen larabawa na yankin tekun da sauran makobta.
Taron ya hada da ministan kudi na kasar Saudiya, gwamnann babban bankin kasar, da kuma wadanda suke ruwa da tsaki a harkkin kasuwanci na kasar ta saudia, sun hadu da tokwarorinsa na Iran inda suka tattauna kan al-amuran tattalin arziki a tsakaninsu.
Himmati ya bukaci karin hadin kai da kasar saudiya don zuba jari a fannoni daban-daban a kasar Iran. Har’ila yau sun tattauna batun harkokin kudade a lokacin ayyukan hajji.