Iran: Harin IRGC Kan Isra’ila Martanin Kisan Haniyyah, Nasrallah da Nilforoshan Ne

 Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa: ta kaddamar da hare-hare da manyan makamai

 Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa: ta kaddamar da hare-hare da manyan makamai masu linzami kan Isra’ila, domin mayar da martani kan kisan Ismail Haniyyah, Sayyid Hassan Nasrallah da Janar Abbas Nilforoushan.

Tun kafin wannan lokacin dai Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kisan Isma’ila Haniyya wanda Isra’ila ta yi kisan gilla a Tehran, inda Iran din ta ce za ta mayar da martanin ne a wuri da kuma lokacin da tag a ya dace.

A ranar Juma’ar da ta gabata kuma Isra’ila ta kai hare-hare a kudancin birnin Beirut, wanda ya yi sanadin shahadar Sayyid Hassan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah, gami da janar Abbas Nilforoushan, jami’in IRGC da yake gudanar da ayyukansa na bayar da shawarwaria  Lebanon.

Iran ta kara jaddada cewa dole ne Isra’ila ta fuskanci sakamakon abin da ta aikata na ta’addancin kisan Sayyid Hassan nasrallah da kuma jami’in na IRGc da sauran manyan kwamandojin Hizbullah, da kuma fararen hula da ba su ji ba su gani ba.

An yi ta jin karar fashe-fashe a ko’ina a yankunan Falastinu da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye,  yayin da kafafen yada labaran Isra’ila suka ce Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami kan yahudawan sahyuniya na Isra’ila.

An ga saukar  makamai masu linzami a sararin samaniyar Tel Aviv kuma ana iya jin karar fashewar wasu abubuwa a birnin al-Quds da aka mamaye, lamarin da ya sa yahudawa yan share wuri zauna suka tsere zuwa matsugunnai.

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Isra’ila ta ce ba za a bari wani jirgin sama ya tashi ko ya sauka a dukkan filayen jiragen saman Isra’ila ba.

Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta ba da rahoto “kai tsaye” daga yankunan Negev, Sharon da sauran wurare a lokacin kaddamar da harin na Iran.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun fitar da sanarwa jim kadan bayan an kai harin da manyan makamai masu  linzami.

Sanarwar ta ce, a matsayin martani kan shahadar shugaban Hamas Isma’il Haniyah, da shugaban Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kwamandan IRGC Abbas Nilforoushan, rundunar sojojin saman IRGC ta harba makamai masu linzami da dama da suka nufi wasu muhimman sansanonin soji da na leken asiri a tsakiyar yankunan Falastinu da yahudwa suka mamaye.

Rundunar ta IRGC ta ci gaba da cewa, harin ya yi daidai da ‘yancin kasar na samun halaltacciyar kariyar kai kamar yadda kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya ya tanada, da kuma mayar da martani kan  karuwar laifuffukan da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa tare da cikakken goyon  Amurka, a  kan al’ummar Lebanon da Gaza.

Rundunar IRGC ta kara da cewa gwamnatin sahyoniyawan za ta fuskanci karin munanan hare-hare idan har ta mayar da martani kan wadannan hare-hare da aka kai kanta daga Iran.

Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, harin makamai masu  linzami martani ne halastacce wanda dukkanin dokokin kasa da kasa suka amince da shi kuma suka halasta shi, kuma ya yi daidai da hankali da kuma abin da ya dace a kan gwamnatin Sahyuniya ta Haramtacciyar kasar Isra’ila.

Har ila yau, rundunar IRGC ta sake maimaita gargadi ga gwamnatin yahudawan da cewa, za ta fuskanci wasu hare-haren mafi muni idan ta yi gigin daukar matakin martani ko yin wani shishigi a kan kasar Iran.

Jim kadan bayan kaddamar da harin na Iran a kan Isra’ila a daren wannan Talata, al’ummomi a ko’ina a cikin kasashen Iraki, Yemen, Lebanon da Falastinu da ma wasu kasashen musulmi da na larabawa, sun fito a kan tituna suna ta murna tare da jinjinawa dakarun IRGc na kasar Iran kan daukar matakin ladabtar da Isra’ila da ta dauka, ta hanyar yi mata ruwan daruruwan manyan makamai masu linzami, a daidai lokacin da Isra’ila take fankama da takama da girman kai saboda ganin irin goyon bayan da take samu kai tsaye daga Amurka da wasu gwamnatocin manyan kasashen turai masu hidima ga yahudawan sahyuniya.

Masa kan harkokin tsaro da siyasar kasa da kasa a yankin gabas ta tsakiya da ma wasu kasashen duniya sun yi imanin cewa, harin na Iran ya zo daidai lokacin da ya dace, a lokacin da Netanyahu ke ikirarin cewa zai sauya fasalin siyasar yankin gabas ta tsakiya a cikin izgili, biyo bayan kisan Sayyid Hassan Nasrullah, inda yake kallon tamkar wata babbar nasara a gare shi wadda za ta bas hi damar cin karensa babu babbaka a kan dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma harin na Iran na a matsayin wata babbar amsa ce ga fankama da tinkahon da Netanyahu yake a yi bayan kisan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments