Iran : Hare-haren da Isra’ila ta kai kan Yemen babban laifin yaki ne

Iran ta yi kakkausan suka game da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasar Yemen tana mai danganta su da babban laifin

Iran ta yi kakkausan suka game da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasar Yemen tana mai danganta su da babban laifin yaki.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kai wa kan ababen more rayuwa na tattalin arzikin kasar Yemen da kuma cibiyoyin jama’a sun zama “laifi na yaki da cin zarafin bil’adama.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar, Esmail Baghai ya yi kakkausar suka kan hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kaiwa kan manyan tashoshin jiragen ruwa na kasar Yemen.

Ya kara da cewa hare-haren da aka kai a tashar jiragen ruwa ta Hudaydah, Ras Issa da kuma Salif na kasar Yemen, ya zama babban cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.

Mista Baghai Ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila tana kai irin wadannan hare-hare ne a daidai lokacin da al’ummar kasar Yamen ke fama da matsanancin hali na jin kai.

Kakakin ya jaddada cewa Amurka da Birtaniya da wasu kasashen yammacin duniya suna da hannu a ci gaba da aikata laifukan da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma ta’addancin da take yi kan kasashen musulmi a yankin.

Ya jaddada cewa goyon bayan da kasashen yammacin duniya ke baiwa Isra’ila, ya kara bai wa gwamnatin Isra’ilar karfin gwiwa wajen aiwatar da hare-haren wuce gona da iri da kisan kiyashin da take yi wa mata da kananan yara na Falastinawa wadanda ba su da kariya, kuma a halin yanzu  ga al’ummar Yemen da ake zalunta.

Jami’in na Iran ya kuma soki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da yin shiru a kan hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke yi, Ya kara da cewa: Dole ne al’ummar musulmi su tashi tsaye wajen yakar zaluncin da gwamnatin ke yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments