Shugaban cibiyar fasaha da kere-kere ta Pardis a nan Tehran ya bada sanarwan cewa, wakilai daga kasashe 65 ne suka bayyana anniyarsu ta halattan gasar fasahar kere-kere ta shekara ta 2025 a cibiyarsa.
Kamfanin dilancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Mehdi Saffaari –Nio yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa gasar ta dai-dai kun mutane, wadanda zasu gwada korewarsu da kuma fasahar da suke da ita a gasar wacce za’a gudanar daga ranar 27-30 ga watan Octoba damukeciki a nan Tehran.
A taron yan jaridun da ya kira don bada wannan sanarwan Mehdi Safaari-nio ya ce mafi yawan mahallata gasar matasa ne musamman daliban makarantu wadanda suke son gwada korewarsu da kumailminsu. Kuma a cikin irin wannan gasar ne suke gane matsayinsu da kuma yawan ilmi ko fasahar da suke da shi.
Wannan shi ne karo na biyu wanda cibiyar Fasahar kere-kere ta Pardis take shirya gasa irin wannan.
Ya ce a gasar ta bana za’a gwada korewar mahallat fiye da 1000 daga cikin gida da kuma kashe kimani 65. A fannonin kirkirerren fasaha (IA), fasahar Internet, robot, tsaron a yanar gizo.