Iran: Dangantaka Tsakanin Landan Da Tehran Za Ta Kyautata Ne Kawai Idan Birtaniya Ta Gyara Halinta

Jakadan kasar Iran a birnin London ya bayyana cewa dangantaka tsakanin Iran da burtania zai kyautata ne kawai idan gwamnatin kasar Burtania ta gyara halayenta.

Jakadan kasar Iran a birnin London ya bayyana cewa dangantaka tsakanin Iran da burtania zai kyautata ne kawai idan gwamnatin kasar Burtania ta gyara halayenta.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto jakadan JMI a birnin London Ali Mousawi yana fadar haka a faren jiya Alhamis a jawabinda da ya gabatar a taron bikin cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran.

Musavi ya kara da cewa, juyin juya halin musulunci wanda ya sami nasara a kasar Iran a ranar 11 ga watan Fabrayrun shekara ta 1979 ya samo asaline daga son yenci da ci gaba na mutanen kasar Iran na shekaru aro aro sannan an gina su gaba daya kan karantarwa addinin musulunci.

Taron wanda aka gudanar da shi a birnin London ya sami halattan jami’an ma’aikatar harkokin waje na kasar Burtaniya. Jakadun wasu kasashe a birnin Londan, malaman Jami’o’ii dalibai da kuma yan kasuwa da sauran mutane.  

Bikin cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran a wannan karon dai ya zo a dai dai lokacinda kasar take dak da shiga yaki da Amurka da kuma HKI a yankin gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted