Sojojin ruwa na kasashen Rasha da JMI zasu fara atisayen sojojin ruwa na hadin giwa a tekun Caspian a makon mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na Iran ya bayyana cewa atisayen sojojin ruwa na kasashen biyu zai fara ne a yau Litinin 21 ga watan Yuli na wannan shekara. Kuma an sanya masa suna CASAREX2025, kuma zai ci gaba har na kwanaki uku.
Labarin ya kara da cewa sojojin ruwa na arewacin kasar ne zasu shiga atisayen karkashin shi’arin hadin kai don tabbatar da zaman lafiya da tsaron tekun Caspian.
Har’ila yau bangaren sojojin ruwa na IRGC zasu shiga atisayen a yayin da sojojin ruwa na tarayyar Rasha zasu shiga atisayen.
Wannan atisayen yana daga cikin shirin kasashen yankin tekun Caspian na ceto da kuma aikin tabbatar da tsaron tekun.