Search
Close this search box.

Iran da Rasha sun jaddada wajabcin karfafa hadin kai bisa dabaru, tuntubar juna akai-akai

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Rasha su karfafa hadin gwiwa bisa

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Rasha su karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare kan abubuwan da ke faruwa a yankin.

Bagheri Kani ya yi wannan tsokaci ne a wata ganawa da ya yi a birnin Tehran a ranar Lahadi da Igor Khovaev, wakilin musamman na ministan harkokin wajen kasar Rasha kan batutuwan tallafawa daidaita huldar dake tsakanin kasashen Armeniya da Azabaijan.

Ya ce kamata ya yi Tehran da Moscow su ci gaba da tuntubar juna bisa la’akari da mahimmancin abubuwan da ke faruwa a yankin Caucasus da kuma kara tsoma bakin kasashen waje kan harkokin yankin.

Ya kara da cewa, bangarorin biyu suna da matsaya da muradu guda kan jagorancin al’amuran shiyya-shiyya da na kasa da kasa, ciki har da yankin Caucasus.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata matsayin kasar kan mahimmancin daidaita al’amura a yankin ta hanyar lumana.

Bagheri Kani ya ce yana da matukar muhimmanci a yi amfani da hanyoyi kamar tsarin hadin gwiwa na 3+3 domin warware matsalolin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments