Iran Da Pakistan Sun Amince Da Ninka Kasuwancin Kayakin Noma A Tsakaninsu

Gwamnatocin kasashen Iran da Pakisatan sun amince su ninninka yawan kayakin noma na kasuwanci a tsakaninsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto

Gwamnatocin kasashen Iran da Pakisatan sun amince su ninninka yawan kayakin noma na kasuwanci a tsakaninsu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto minitan noma na kasar Iran Jihad Gholam reza Nouri yaqna fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa kasashen biyu zasu karfafa harkokin siyasa da kuma tattalin arziki tsakaninsu, inda suke son ya kai dalar Amurka billiyon $3 daga biliyon $1.4 da yake a halin yanzu. Ya ce suna saran zsu kai wannan adadin a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Nouri ya bayyana haka ne bayan ya gana da Rana Tanveer Hussain  Na ma’aikatar cibiyar binciken na ayyukan noma na kasar Pakisatan a nan birnin Tehran. Ya ce idan wannan shirin ya kankankama to Iran zata dogara da makobciyarta ta gabas waje samun masara da nama .

Yace banda masara da da shinkafa ira+n zata shigoda kasha 60% na naman da take bukata daga kasar Pakisatan, sannan Iran kuma a nata banagren zata fito da albarkatun tabbobi, wadanda suka hada da madara, man shanu, har’ila yau da yayan itace, da kwayoyi kamar tin da zaitun da kayan marmari da ganyayyaki kamar su salat da sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted