Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10.
Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a kasar ta Pakistan. Ya kuma ce dole ne shuwagabannin kasashen biyu tsara yadda hakan zai kasance.
Muqaddam ya kuma kara da cewa gwamnatocin kasashen biyu suna da dangantaka ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da kasuwanci, al-adu, addini da tsaro da sauransi.
Cibiyar kasuwanci da kuma kamfanoni a kasar Pakistan yana daga cikin cibiyoyin kasuwanci mafi girma a kasar ta Pakistan.
Daga karshe Jakadan ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arziki mafi munin da gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Iran amma ta aiwatar da harkokin kasuwanci da kasashen yankin musamman kasar Pakistan.