Kasashen Mexico da Iran sun yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Ofishin jakadancin Iran da ke Mexico ya yi watsi da “iƙirarin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi game da wargaza wani makircin da Iran ta shirya na kashe jakadan Isra’ila a Mexico.”
A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Iran ya bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙirƙirar kafofin watsa labarai da kuma ƙarya bayyananna da nufin lalata dangantakar abokantaka da tarihi tsakanin ƙasashen biyu (Mexico da Iran),” yana mai jaddada kin amincewa da ikirarin tare da bayyana shi a matsayin makircin makiya a fili.
A nata ɓangaren, hukumomin Mexico sun fitar da wata sanarwa suna cewa: “Ba su da wani rahoto game da wani yunƙuri da ake zargin an yi wa jakadan Isra’ila a Mexico na neman kashe shi.”