A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da takwaransa na kasar masar Badr Abdelatty sun bayyana cewa isra’ila na ci gaba da kai hare-hare da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza da kuma kasar labanon,
Ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai mataki 20 kan gaza,wanda shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar hujja ce da ta tabbata tun daga farko kamar yadda rahotanni da suka fito daga yankin gaza suka bayyana cewa akalla mutane 366 ne abin ya shafa daga lokacin da aka cimma yarjejeniyar zuwa yanzu.
A watan nuwamba shekara ta 2024 ne aka cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin kungiyar hizbulla da HKI bayan hare haren da isra’ila ta kai , da yin kisan kare dangi kan alummar gaza a watan oktoban shekara ta 2023
An tilastawa Isra’ila kulla yajejeniyar ce bayan kashi da ta sha a hannu hizbullah inda ta yi mummuna asara a filin daga, ta kasa cimma burinta bayan kashe mutane fararen hula 400 a kasar labanon.
Haka zalika ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayi game da dangantar dake tsakaninsu kuma sun amince a ci gaba da tattaunawa sosai kan yadda za su kara fadada dangantakar dake tsakani