Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa.
Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi kasar Labanon, tare da jaddada muhimmancin kiyaye yanayin amincewa da daidaito tsakanin bangarori daban-daban na siyasa, da kuma kaucewa duk wani mataki da zai iya haifar da rikici a cikin gida.
Bangarorin biyu sun jaddada bukatar janyewar haramtacciyar kasar Isra’ila gaba daya daga yankunan da take ci gaba da mamayewa a kudancin kasar Lebanon da kuma dakatar da kai hare-hare a kan mutanen kasar.