Iran da china Za su Yi Bikin Cika Shekaru 55 Da Huldar Diplomasiya Tsakaninsu

Adai dai lokacin da bikin cika shekaru 55 na kulla hulda diplomsiya tsakanin Iran da China ke kara karatowa ta , dukkan kasashen biyu suna

Adai dai lokacin da bikin cika shekaru 55 na kulla hulda diplomsiya tsakanin Iran da China ke kara karatowa ta , dukkan kasashen biyu suna kokarin ganin sun kara karfafa alakar dake tsakaninsu , Ambasado Ahmad Fazli ya jaddada game da muhimmancin karfafa dangantaka a mataki na kasa da kasa, bisa hangen nesa da girmama juna.

Ganawar da aka yi tsakanin jakadan kasar iran a bejin Rahmani Fazli da Miao Deyu matakimakin ministan harkokin wajen kasar china ta nuna aniyar kasashen biyu na kara karfafa dangantakarsu ta dogon lokaci.

A lokacin ganawar da mataimakin ministan harkokin wajen kasar china rahmani ya jadda muhimmancin kara dankon zumunci tsakanin iran da china, musamman ma yin muhimmacin aiki tare a yankin,  don haka bikin cika shekara 55 zai zama wata damace da zaa kara fadada dangantaka da yin aiki tare

Bangaren iran a shirye yake yayi aiki da kasar china don karfafa muamala  da zurfafa yin aiki tare a bangarori daban daban bisa yarjejeniyar da shuwagabannin kasashen biyu suka cimma matsaya akai,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments