Iran da Amurka zasu tattauna dangane da shirin kasar Iran na makamashin Nukliya a birnin Istambul na kasar Turkiyya, a dai dai lokacinda Amurka ta yi wa kasar Kawanyya da makamanta daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kamfanin dillancin labaran Reuters a jiya Litinin, kuma Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ne zai wakilci JMI a tattaunawar a yayinda Steve Witskoff mai bawa shugaban kasar Amurka shawara a kan al-amuran gasab ta tsakiya zai wakilci gwamnatin Amurka a tattaunawar.
Wasu majiyoyin kasashen biyu sun bayyana cewa wakilai daga kasashen Qatar, saudia, UAE da kuma Masar zasu halarci taron wanda za’a gudanar a ranar Jumma’a mai zuwa. Sannan tattaunawar zata kasashen tsakanin Iran da Amurka da kuma wasu daga cikin wakilan kasashen yankin.
Wannan yana faruwa ne kwanaki biyu kacal da sanarwan da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran wato Dr Ali Larijana ya bada sanarwan cewa an fara shirin ganawa tsakanin Iran ta Amurka kan wasu al-amuran da suke tsabani a tsakaninsu.
Kafin haka dai jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminaei ya jakunnen Amurkan cewa cewa a wannan karon idan ta kuskura ta fara yaki to kuwa zata hada duk da dukkan kasashen yankin ne.