Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta bada sanarwan cewa kasar Iran ce a gaba da dukkan kasashen makobta da kasar Afganisatan wacce tafi shigo da kayakinta cikin kasar a shekara ta 1403 ta kalandar Iraniyawa da ta kare.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan Abdussalam Jawad Okhande-Zadeh ya na fadar haka a yau Lahadi:
Ya kuma kara da cewa, kasashen da suka shigo da kayaki a kasar Afganistan a shekarar da ta gabata sun hada ta Iran, a gaba da ko wace kasa, sannan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Pakisatn, China da kuma Turkamanistan.
Kakakin ma’aikatar kasuwancin ta kasar Afganisatn ya ce a dayan bangaren kuma kasar Afaganista ta fidda kayaki zuwa kasashen waje wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka biliyon guda a shekarar da ta gabata, kuma sun hada da busassun yayan itace, da darduma, da awduga da duwatsu masu daraja.