Iran : An bude taron kasa da kasa na cikar kwanaki 40 da shahadar Sayyid Nasrallah

A Iran an bude wani  taron kasa da kasa mai lakabi da  “Maktab Nasrallah” a birnin Tehran domin cika kwanaki 40 da shahadar jagoran gwagwarmaya

A Iran an bude wani  taron kasa da kasa mai lakabi da  “Maktab Nasrallah” a birnin Tehran domin cika kwanaki 40 da shahadar jagoran gwagwarmaya kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah.

Taron na samun halartar malamai daga kasashe 13 da suka hada da Lebanon, Iraki, Bahrain, Masar, Kuwait, Turkiyya, Indiya, Malaysia, Aljeriya, da Tunisia.

haduwar wadda ma’aikatar al’adu ta shirya, na nazari kan bangarori daban-daban na tarihi, siyasa na Nasrallah.

Batutuwan da aka tattauna sun hada da halayensa na kashin kai, tsayin daka da ya yi da yahudawan sahyoniya da mulkin mallaka, da hangen nesansa na sabuwar wayewar Musulunci.

Manyan mutane da dama da suka halarci taron sun hada da Ayatollah Alireza Arafi, ministan al’adu da Seyed Abbas Salehi, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi, mataimakin shugaban kasar mai kula da tsare-tsare Mohammad Javad Zarif, da Manjo Janar Ismail Qaani, kwamandan dakarun Quds.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments