Iran : Amurka Da Isra’ila Ne Suka Kitsa Abinda Ke Faruwa A Siriya

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa Amurka da Isra’ila suka kitsa abinda ke faruwa a Siriya. Ayatullah

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa Amurka da Isra’ila suka kitsa abinda ke faruwa a Siriya.

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da wani gungun jama’a daga bangarori daban-daban, yau Laraba.

Babu shakkar cewa tushen abin da ya faru a Siriya an shirya shi ne a dakin kwamandojin Amurka da Isra’ila.”

Jagoran ya ce abin da ya faru a kasar Siriya wani shiri ne na hadin gwiwa na Amurka da yahudawan sahyoniya, duk da cewa wata kasa da ke makwabtaka da ita ma ta taka rawa.

Ayatullah Khamenei ya yi watsi da rade-radin da ake yi game da raunin da bangaren ‘yan gwagwarmaya ke samu bayan da mayakan suka mamaye babban birnin kasar Siriya.

Jagoran ya kuma yi watsi da rade-raden cewa lamarin zai yi wa Iran rauni.

Masu fadin hakan sun jahilci lamarin, kuma da yardar Allah, Karin Iran, da Musulmi da ‘yan gwagwarmaya zai kara girma ne kawai inji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments