Kwamandan sojan na Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi.
Birgediya janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda za mu yi aiki da su a kodayaushe.
Kwamandan sojan saman na Iran ya kara da cewa; A halin da ake ciki a yanzu sojan saman Iran suna da karfi sosai, sun kuma dogara ne da kansu wajen kera abubuwan da suke da bukatuwa da su.
Har ila yau Birgediya Janar Hamid Wahidi ya ce, yana alfahari da dukkanin abokan aikinsa sojojin sama masu jarunta wadanda su ka tabbatar da hakan a lokacin farmakin “Wa’adus-sadiq”. Haka nan kuma ba za su taba ja da baya ba a karkashin kowane yanayi.