Search
Close this search box.

Iran: A ranar 5 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu

A ranar 5 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar Iran, bayan da dukkanin ‘yan takarar

A ranar 5 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar Iran, bayan da dukkanin ‘yan takarar shugabancin kasa a zaben ranar Juma’a suka kasa samun kasha 50m cikin dari na dukkanin kuriun da aka kada.

Mohsen Eslami, kakakin hedkwatar zaben kasar ne ya sanar da sakamakon karshe a wani taron manema labarai bayan sanar da kidaya kuri’u na karshe.

Ya ce daga cikin kuri’u miliyan 24.5 da aka kada, tsohon ministan lafiya kuma dan majalisa Masoud Pezeshkian ya samu miliyan 10.4 yayin da tsohon mai shiga tsakani kan batun nukiliyar kuma babban jami’in tsaro Saeed Jalili ya samu miliyan 9.4.

Sauran biyun kuma wato kakakin majalisar Mohammad Baqer Qalibaf da tsohon ministan harkokin cikin gida Mostafa Pourmohammadi – sun biyo bayan mutane miliyan 3.3, da kuma  206,000 bi da bi.

Pezeshkian da Jalili za su fafata a zagaye na biyu na zaben da za a yi ranar 5 ga watan Yuli. Ana zuwa zagaye na biyu ne idan babu dan takara da ya samu kashi 50 cikin 100 na kuri’un da aka kada baki daya.

Ministan cikin gidan kasar Ahmad Vahidi ya ce gwamnati a shirye ta ke ta gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba,  kamar yadda kuma ya yabawa al’ummar kasar da hukumomin zabe da suka gudanar da zaben ba tare da wani cikas ba.

Ya  ce, An gudanar da zabukan cikin aminci da kwanciyar hankali, an yi takara mai tsanani da kuma fitowar jama’a a  rumfunan zabe,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai bayan kammala kidaya kuri’u.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments