Indonesia: Tawagar Iran Tana Halartar Taron Majalisun Kungiyar  Kasashen Musulmi

‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi. A yau

‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi.

A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19.

Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.”

 Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari.

Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a wurin taron, akan batutuwan da su ka shafi siyasa, al’adu, mata da iyali.

A yayin wannan taron za a tabo batun da ya shafi al’ummar Falasdinu da halin da suke ciki,musamman a yankin Gaza.

A gobe Talata kuwa shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Kalibaf zai isar birnin na Jakarda domin halartar taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments