Human Rights Watch Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Rusa Makarantu Fiye Da 500 A Gaza

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa makarantu sama da 500 a Gaza A

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa makarantu sama da 500 a Gaza

A cikin wani sabon rahoton da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar, kungiyar ta zargi sojojin mamayar Isra’ila da kai hare-hare ba bisa ka’ida ba kan makarantun da ke suka zame mafakar ‘yan gudun hijira a zirin Gaza tun daga watan Oktoban shekarar 2023, inda suka kashe daruruwan Falasdinawa fararen hula.

A cikin rahotonta da ta fitar yau Alhamis, kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bayyana wadannan hare-haren a matsayin nuna wariyar al’umma, kuma kan iya kai wa ga laifukan yaki. An yi nuni da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila suna yin amfani da makaman da Amurka ta kera, kuma suna kai hare-hare domin kara kashe Falasdinawa fararen hula da kuma masu gudanar da ayyukan ceto baya ga wadanda suke jikkata.

Kungiyar ta yi rubuce-rubucen game da kai hare-hare kan makarantu sama da 500 a duk fadin zirin Gaza da suka rikide zuwa mafakar ‘yan gudun hijira, wanda ke nuna irin rashin kula da rayukan fararen hula.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments