Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya “OCHA: ta bayyana cewa:Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da hanawa tare da janyo cikas na shigar agaji cikin Gaza
Ofishin Hukumar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya “OCHA” da ke Gaza ya bayyana cewa: Mahukuntan gwamnatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da hanawa tare da dakile mafi yawancin tawagogin kungiyoyin ayyukan agajin jin kai gudanar da ayyukansu a duk fadin Zirin Gaza.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniyan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a ya bayyana cewa: A cikin bukatu 12 da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar na neman daidaita ayyukan jin kai da aka gabatar a ranar Laraba, an yi watsi da bukatu 6 kai tsaye, yayin da aka yi watsi da guda 3 daga masu shirya taron saboda kalubalen tsaro da wasu matsaloli, yayin da aka amince da bukatar daya kacal, amma ita ma tana fuskantar cikas da yawa daga gwamnatin mamayar Isra’ila, sannan wasu 2 da aka sauƙaƙe gudanar da su kuma ake aiwatarwa.
Hukumar “OCHA” ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi watsi da yunkurin kai agajin jin kai zuwa yankunan arewacin Zirin Gaza da ta killace.