Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar

Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar,

Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar, daga karshe dai hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta najeriya ta ci tarar kamfanin naira miliyan 5 saboda kate dokokin da suka shafin fasinjojinta.

An fitar da wannan sanarwa ce a shafin x na micheal achimugu daraktan kula da hulda da jama’a da kula da fasinjoji, ya kara da cewa wannan hukumci ya sanya adadin kamfanonin jiragen sama da aka ci tara sun kai guda 7 a wannan shekarar ta 2025

Hukumar NCAA ta zargi kamfanin jiragen sama na Qatar airways a watan satumban shekarar da muke ciki da take dokokin kula da hakokin    fasinjoji da kuma yin mummunar muamala da fasinjonin ta yan najeriya

Haka zalika hukumar ta yi Gargadin kakabawa kafanin jirgin saman takunkumi idan ya ci gaba da keta dokokin hukumar jiragen sama ta kasar. Hukumar ta ta bayyana cewa a 28 ga watan decembar shekara ta 2024 ta sanya takunkumi kan kamfanin jiragen sama na air peace, Ethiopian airline, Arik Air, Aero contractos da kuma royala air maroc saboda taka dokokin hukumar da ta gindaya a bangare na 19.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments