Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD Ta Ce Sauye-Sauyen Da Ke Faruwa A Amurka Zai Shafi Al-Amura Da Dama A Majalisar

Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD.

Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD.

Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za su shafi al-amura da dama a cikin gida da kuma sauran kasashen  duniya.

Volker Turk ya ce  al-amura da suka shafi nuna wariya ne, mai yuwa su zama akasin haka nan gaba, bayan wadannan sauye sauye sun fara aiki.
Wannan dai shi ne jawabi mai muhimmancin da wani jami'an MDD ya gabatar dangane da abubuwan da ke faruwa a sabuwar gwamnatin Amurka. 
Turk ya kuma kara da cewa tasirin sauye-sauyen zasu kara bayyana nan gaba, a lokacinda matakan da gwamnatin Amurka ta Donal Trump ta fara aiwatar da su a kasa.
 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments