Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Francesca Albanese tana fadar haka a shafinta na X a jiya Litinin. Ta kuma kara da cewa an kashe mutane da yawa, kuma an kashe yara da yawa. An kona su da ransu, a cikin makarantar inda suke mafaka a ciki.
Albanese ta hada da hotunan bidio wanda suke nuna irin yadda wuta take kona Falasdinawa a cikin makarantar, ta turasu a shafin nata. Ta kara da cewa dole ne mu tsaida wuta a gaza kuma falasdinawa su gafarta mana kan cewa mun kasa yin haka har abin ya kai wannan matsayin.