Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya ta yi tsananin gargadi game da kisan da ake yi a El-Fasher dake arewacin Darfur na kasar Sudan, ya bayyana birnin da cewar yana cikin mummunan yanayi da kuma karuwar hare-hare mafi muni a kwanaki 10 da suka gabata,
Yankin El-Fasher yana kasancewa daya daga cikin garuruwan dake fuskantar mummunan yanayi na zubda jinni a fadin kasar Sudan, da kuma rikice-rikicen kabilanci da kai harin kan fararen hula, kuma yana barazanar karuwar rarrabuwar kai a kasar da tsawaita yakin da jawo kashe dubban mutane da kuma raba miliyoyi da gidajensu,
Tun a watan aprilun shekara ta 2023 sojojin Sudan da dakarun sa kai na kungiyar RSF suka tsunduma cikin kazamin yaki ,a ranar 26 ga watan oktoba kuma kungiyar RFS ta kwace ikon kula da yankin El-fasher inda kungiyoyin ciki da wajen kasar suka bada tahoton irin kisan kare dangi da aka yi wa fararen hula a garin
Hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya tana kara matsin lamba kan kasashen duniya da su dauki matakin kare rayukan fararen hula a garin.