Jagoran kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta Yemen, Abdul-Malik al-Houthi ya ce tura jiragen ruwan yakin Amurka ba zai iya hana sojojin Yemen kaddamar da farmakin mayar da martani ga Isra’ila ba bayan harin da ta kai kan lardin Hudaidah da ke yammacin kasar.
‘Yan gwagwarmaya sun kuduri aniyar mayar da martani ga kisan gillar da Isra’ila ke yi, amma Amurka na ta iyakacin kokarinta, da kuma bi ta hanyoyin siyasa, don hana martanin kungiyoyin, game da kashe-kashen Isra’ila,” in ji Houthi a wani jawabinsa a yammacin yau Alhamis.
Shugaban na Ansarullah ya ce ramuwar gayya na nan gaba, ba fashi.
Ya ce sojojin ruwan Yemen za su ci gaba da kai hare-hare ta ruwa a kan jiragen ruwan ‘yan kasuwa da ke da alaka da Isra’ila a cikin tekun bahar maliya domin tallafa wa Falasdinawa a zirin Gaza.
Houthi ya ce, “Muddun hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza zasu ci gaba, to za suma zasu ci gaba da gudanar da ayyukan soji,” in ji Houthi, yana mai bayyana hare-haren da sojojin Yamen ke yi na nuna adawa da Isra’ila a matsayin wani aiki na addini da nuna goyan bayan ga al’ummar Palasdinu.
Har ila yau shugaban na Ansarullah ya yi watsi da jibge sojojin Amurka da jiragen ruwa na yaki a wasu kasashen Larabawa na yankin yammacin Asiya, yana mai cewa irin wadannan matakan ba za su iya hana sojojin Yemen su kaddamar da farmakin ramuwar gayya ba bayan harin da aka kai a lardin yammacin kasar na Hudaidah a watan jiya.