HKI Tana Cigaba Da Keta Tsagaita Wutar Yaki A Lebanon

A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai

A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai hare-hare a yankunan Jenta da Biqa.

Tashar talabijin din ‘almanar ta watsa labarin da yake cewa; Jiragen yakin abokan gaba ‘yan sahayoniya sun kai hare-hare har sau uku a yankin al-sha’arah’ dake gabashin Jenta a Biqa.

Da marecen jiya Alhamis din dai jiragen yakin HKI sun yi shawagi a kasa-kasa yankin Biqa, kamar kuma yadda sojojin nasu su ka jefa bama-bamai masu haske a yankunan Kafar-Shuba, dake kudancin Lebanon.

Irin wadannan keta tsagaita wutar da sojojin HKI suke yi, yana sanya alamar tambaya akan aikin da kwamitin dake kula da tsagaita wutar yakin yake yi.

Tun bayan da wa’adin ficewar sojojin HKI ya yi, sun ki ficewa tare da kafa wasu wuraren bincike na soja guda biyar da suke ci zaga da zama a cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments