HKI Tace Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Kaiwa Kasar Hare Hare Har Sau 163 A Cikin Wannan Watan Kadai

Kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa dakarun kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun kai hare hare kan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye

Kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa dakarun kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun kai hare hare kan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye har sau 163 a cikin watan satumban da muke ciki kadai.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa hare haren kungiyar kan HKI a wannan watan ya fi tsanani idan an kwatanta da watannin baya. Kuma da alamun yawan hare haren karuwa suke.

Hare haren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon kan arewacin HKI dai sun tilastawa yahudawa mazauna yankin arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye da dama kauracewa gidajensu.

An kiyasta cewa yahudawa kimani dubu 230 ne suka kauracewa gidajensu tun bayan fara yakin tufanul Aksa watanni 11 da suka gabata.

Kungiyar Hizbullah dai ta shiga yaki da HKI ne tun ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2023 don tallafawa falasdinawa a gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi dare dare. Amma kuma takan maida martani kan HKI a duk lokacinda sojojinta suka kai hare hare a kudancin kasar ta Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments