HKI Ta Yi Furuci Da Gajiyawa A Gaban Hizbullah Ta Lebanon

Jami’an HKI sun yi furuci da cewa sun gajiya wajen dakatar da hare-haren da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon take kai musu. Mazauna sansanin yahudawa

Jami’an HKI sun yi furuci da cewa sun gajiya wajen dakatar da hare-haren da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon take kai musu.

Mazauna sansanin yahudawa ‘yan share wuri zauna na “Kiryat Shimona” sun bayyana cewa, ba su da wata hanya da za su iya yin mafani da ita domin hana hare-haren da ‘yan gwgawarmaya daga Lebanon.

Tun fara kai wa Gaza hari da ‘yan sahayoniya su ka yi ne, Hizbullah ta shiga taya wa Falasdinawa fada, ta hanyar kai wa sansanoni da cibiyoyin soja da na leken asirin HKI hare-hare.

Magajin garin na “Kiryat Shimona” Afkhay Astrin, ya furta cewa; Salon hare-haren na Hizbullah ya rikita sojojin HKI da kasa sanin yadda za su fuskance shi.

Shi kuwa janar Amus Gil’ad mai murabus cewa ya yi, Arewacin Isra’ila ya zama kufai saboda hare-haren na Hizbullah.

Wani jami’in mai kula da matsugunin ‘yan share wuri zauna na                    “ Mirgiliout’ ya ce,Harkokin tattalin arziki sun durkushe a wurinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments