Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu.
Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne.
Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa. 54 kuma an dauresu na lokaci mai tsawo, mai yuwa wasunsu ba zasu rayuwa zuwa karshen hukuncin da aka yanke masu ba. Kuma yahudawan suna azabtar da wasu Falasdiwa kafin ta sallamesu.
Labarin ya kara da cewa yanhudawan sun hana falasdinawa zuwa kusa da inda gidan kasan Ofer yake, don kada su tarbi fursinoninsu, su kuma gudanar da bukukuwan farin ciki a can ba.