Gwamnatin HKI ta kama kuma ta tsare akalla yahudawa biyu yan share wuri zauna a yankin yamma da kogin Jordan wadanda take tuhmarsu da yin aikin liken asiri ga jami’an kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an kama yahudawan biyu ne a birnin Qudus kuma an tabbatar da cewa sun aikawa wani Jami’in kungiyar Hizbullah sakonnin wadanda suke bayyana yanayin da yaki yake tafiya a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye. Da kuma yadda yanayin yahudawa suke a cikin kasar a dai-dai lokacinda ake cikin yaki da kungiyar wattani kimani uku da suka gabata.
Abdussalam Qawasimi da Taar Asili dukkaninsu yahudawa larabawan da suke zaune a HKI ne, kum sun aikewa kungiyar hizbullah sakonni ta kafar sadawar ta wattsapp ne, harma daya daga cikindu ya yi magana da sauti da su,
Tuni dai mai gabatar da kara na gwamnatin HKI ya shigar da kara ya na tuhumarsu da laifin aikawa makiya na kasar waje, rahotanni kan yanayin yaki a cikin kasar. Mutanen biyu dai sun aika da hotuna, da kuma hotunan bidiyo wa kungiyar ta Hizbullah a kuma lokacin yaki da ita.