Search
Close this search box.

HKI Ta Amince Da Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Na Kwanaki Uku Saboda A Yiwa Yara Alluran Riga Kafin Cutar Shan Inna

Tashar talabijin ta Aljazeera ta kasar Qatar ta nakalto majiyar HKI na cewa gwamnatin yahudawan ta amince da tsagaita wuta a Gaza na tsawon kwanaki

Tashar talabijin ta Aljazeera ta kasar Qatar ta nakalto majiyar HKI na cewa gwamnatin yahudawan ta amince da tsagaita wuta a Gaza na tsawon kwanaki uku saboda bada dama ga jami’an jinya na MDD wato na hukumar lafiya ta duniya WHO su yiwa dubban yara yan kasa da shekaru 5 alluran riga kafin kamuwa da cutar shan Inna wacce ta bulla a yankin na gaza bayan fara yaki watanni kimani 11 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an dauki fiye da shekaru 25 ba’a sami yaro ko guda dauke da cutar a yankin ba.

Labarin ya bayyana cewa dakatar da bude wutar zai kasance ne na tsawon sa’o’i 8 ne a ko wace rana, har zuwa tsawon kwanaki uku. Sannan za’a dakatar da bude wutar ne daga karfe 6 na safe zuwa 3 na yamma.

Kungiyar Hamas ta ce tana tare da ra’ayin MDD na tsagaita wuta na mako guda wanda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments