A wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta Lebanon ta fitar a jiya Alhamis, ta bayyana cewa, ta kai hari akan sansanin ‘yan share wuri zauna na “Karivot’ a arewacin birnin Haifa, a matsayin taimaka wa mutanen Gaza, da kuma kare kasar Lebanon.
Bugu da kari, kungiyar ta Hizbullah ta kai wani harin da makamai masu linzami akan sansanin bayar da horo na soja da “Iliyakim” wanda yake a kudancin birnin Haifa.
Wasu hare-haren da kungiyar ta Hizbullah ta kai a jiya sun hada akan sansanin ‘yan share wuri zauna na; Hanitah, sai kuma Harmon da Liman. Dakarun na Hizbullah sun yi amfani da makamai masu linzami wajen kai hare-hare akan wadannan sansanonin.
Wani sansanin da shi ma ya fuskanci harin dakarun Hizbullah shi ne na “Shomira” da kuma “Sa’ir” a arewacin Nahariya.
Har ila yau, garuruwan, Safad da Kariyat shimona sun fuskanci hare-hare da makamai masu linzami na dakarun gwgawarmayar Hizbullah.
A yakin kasa kuwa dakarun na Hizbullah sun kai hari akan sojojin mamaya da su ka yi kokarin kutsawa cikin garin “Marun-Ra’as” tare da tilasta musu janyewa da komawa ina su ka fito.
A garin Yarun kuwa, mayakan na Hizbullah sun yi wa ‘yan mamaya kwanton bauna, tare da kashe da kuma jikkata da dama daga cikinsu.
A kusa da yankin kan iyaka na “ Bawwabatu-Fatimah” a garin Kafara-Kalla, dakarun na Hizbullah sun tilasta wa sojojin mamaya janyewa da baya.