Kungiyar ta kasar Lebanon ta fitar da bayani a jiya Litinin tana mai taya al’ummar Falasdinu samun nasara akan ‘yan sahayoniya da masu taimakonsu.
Sanarwar kungiyar ta Hizbullah ta kunshi cewa: Muna taya murna ga al’umma Gaza da al’ummar Larabawa da musulmi da dukkanin ‘yantattu a duniya dangane da wannan gagarumar nasarar da aka samu akan abokan gaba,wanda yake a matsayin Karin dadawa akan tsayin daka da turjiya ta tarihi da Falasdinawan su ka yi a tsawon watanni 15, tun daga farkon guguwar Aksa.
Hizbullah ta bayyana abinda ‘yan gwgawarmayar Falasdinawa su ka yi da cewa abin koyi ne wajen fada da HKI da kuma Amurka da suke yakar al’ummarmu.
Hizbullah ta cigaba da cewa, gwagwarmata ita ce hanya daya wacce za a iya takawa ‘yan sahayoniya birki da ita,kuma abinda ya faru a wannan lokacin cin kasa ne a gare su, wanda zai shiga cikin tarihi.
Bugu da kari kungiyar ta Hizbullah ta ce, lokacin da za a rika yi wa al’umma shita ya wuce, don haka ba za a iya yin galaba ko raunana al’umma ba.
“Jinanen Shahida” Ina ji bayanin na Hizbullah “da kuma tsayin dakar al’ummar Falasdinu mata da maza kananan yara ,haka nan tsofaffi maza da mata su ne ginshikin wannan nasara.”