Hizbullah Ta Maida Martani Ga Ta’asan HKI Da Luguden Wuta Kan Sansanonin Sojojinta

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta maida martani ga hare haren HKI kan wasu wurare a kudancin kasar tare da ruwan makamai masu linzami kan

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta maida martani ga hare haren HKI kan wasu wurare a kudancin kasar tare da ruwan makamai masu linzami kan sansononin sojojin HKI a arewacin Falasdinu da aka mamaye a shekara 1948.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar ta nakalto majiyar kungiyar tana fada a wani bayanin da ta fitar a safiyar yau Litinin. Bayanin ya kara da cewa, da farko mayakan kungiyar sun tawatsa wani taron sojojin yahudawan a Al-Tayhan wanda yake fuskantar kauyen Meis Al-Jabal na kasar Lebanon da sanyin safiyar yau Litinin. Sannan ta sake kai wasu hare haren tare da amfani da makamai masu linzami da kuma atitilari kan barikin sojojin yahudawan a wannan garin.

Labarin ya tabbatar da cewa makaman sun lalata kayakin soje da dama amma babu masaniya kan idan akwai mutuwa da jikatan sojojin yahudawan.

Kafin haka a jiya ma dakarun kungiyar sun kai hare hare kan matsugunan yahudawa a Meula, da kuma wasu kuma kusa da barikin sojoji na Branit. Haka ma makaman Hizbulla sun fada kan

Ruwaisat Al-alam na tuddan Kafarshuba na kasar Lebanon da aka mamaye. Bayanin kungiya ya kammala da cewa sun kai wadannan hare haren ne don tallafawa mayakan Gaza da kuma maida maratani kan hare hare HKI a kan wasu wurare a kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments